Daga: Dr. Aliyu Kankara
Muna kyautata zaton kafin shekarar 1848 babu wani wuri da ake kira Kankara. Bincike ya nuna an kafa garin a cikin shekara ta 1848.
Akwai ra’ayoyi mabambanta a game da dalilin ko mafarin Kankara. A wata ruwaya marar nauyi an nuna unguwa ko wuri na farko da aka fara kafawa a garin da ake kira Tarni ko Kofar Arewa a yau, an nuna cewa fatake ko matafiya a wurin kan tafi daji a gefen yammacin Kankara suna dibar wani abu da ake kira tubata, watau yashi da yake hade da wasu duwatsu da ke dauke da sunadaran karafuna.
To idan suka debo su sai su hada, su sarrafa su yi abaiban da makeran babbaku ke yi, watau kayayyaki da mafarauta ke amfani da su, irin su kwari da baka, mashi, adda, da sauransu da sauran kaysyyakin aikin gida kamar su wuka, takobi, da sauransu.
To, ita tubata, idan an hada ta da yashi, gaba daya ana kiran su Kankara. To ta nan garin ya samo sunan sa, amma a wannan ruwaya
A ruwaya ta biyu, an nuna cewa Kankara ta samo sunan ta daga wasu mutane, malamai da suka fito daga wani wuri ko yanki da ke karkashin kulawar kasar Faskari.
Sun yo gabas a cikin ayari da niyyar tafiya aikin haji, sai suka yada zango a nan Tarni. To kuma sai Allah bai yi nufin su wuce Makkan ba.
Sai suka zauna suka ci gaba da saye da sayarwa a tsakanin su da matafiya da kan yada zango a nan. To wancan yanki da suka fito, an ce sunan sa Kankara, ko Kankaru.
A ruwaya ko ra’ayi na uku wanda ya fi karfi, wanda kuma ya yi kamanni da ra’ayi na biyu, cewa wadannan mutane sun taho zuwa Makka a karkashin jagorancin wani mutum da ake kira Danjammaka. Sai Allah bai yi nufin wucewar su ba, suka zauna nan.
Ita kan ta Kankara Pauwa ta riga ta samuwa.
Ita Pauwa, an kafa ta a cikin shekara ta 1793. Kuma a gefen ta akwai garuruwa da suka riga suka cira kamar su Kurkutawa, Tsafe, Mutu-gwarin-wake, Maidorowa, ‘Yankuzo da sauran su.
A daidai wannan wakati, ‘Yankuzo da Tsafe da Kurkutawa suna a karkashin ikon kasar Katsina, ita kuma Pauwa tana a karkashin kulawar Sokoto.
Akwai ma wani Sarki da ya taba yin mulkin Pauwa ana ce da shi Bello Dabakurau, a Maidorowa ya zauna kafin ya tare Pauwar. Ke nan, a da, Maidorowa ce hedikwatar Pauwa da farko.
Sai daga baya a tsakanin 1915 turawa suka shawarci Sarki Dikko na Katsina da Sarkin Musulmi da su yi musayar kasar su. Aka dauko Pauwa daga Sokoto aka maido da Katsina. Su kuma su Tsafe da ‘Yankuzo aka dauke su daga Katsina aka maishe su a karkashin ikon Sokoto.
Kogo mai Kumaro shi ya fara sarautar Pauwa. Kuma Sarkin Musulmi na wannan lokacin shi ya nada shi. Ya fara sarautar daga 1800. Daga kan sa zuwa na karshe a layin gidan Kogawa an yi sarakuna goma (10).
Na karshe daga cikin su shine Bello Dabakurau, wanda aka yi riginma da shi lokacin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Sabili da ya ce ba za ya yi mubaya’a ba, ba za ya bi Sarkin Katsina ba lokacin da aka fitar da kasar Pauwa daga karkashin kulawar Sokoto ka maido ta kasar Katsina. Dalilin haka sai Sarki Dikko ya fitar da shi, a cikin 1910.
Sai Sarki ya nada Kanwa Nuhu Sarkin Pauwa, wanda ya yi mulki daga wannan lokacin ziwa 1943. Ko da ya ke, a lokacin rabon iyaka wasu al’ummomi da ke kan iyakar Katsina da Sokoto sun rika fashewa suna fantsama cikin kasar Sokoto wai don na su son su bi Katsina. To sai aka rinka aiko Kanwa Nuhu yana kawo masu hatsi da sauran kayan masarufi, wani lokaci har da kidin kashewa. Watau sakon Sarki Dikko. Wannan ya sanya suka zauna.
To kuma Kanwa din Dikko kan aika ya amso haraji a wajen su. Idan wani ya je ba za su ba shi ba. Don haka Razdan na wannan lokacin ya shawarci Dikko da ya tura Kanwa ya rike kasar ta Pauwa.
Da Kanwa ya rasu ran wata juma”a 24/3/1943 sai aka nada dan sa Mamuda, wanda shi kuna ya yu sarautar daga 1943 zuwa 1951 lokacin da aka hutar da shi.
Amma a baya, cikin 1928 Kanwa Nuhu ya komo Kankara da zama saboda Pauwa ta yi lungu, kuma a can ana wahalar ruwan sha.
A cikin 1952 aka nada Alhaji Idris Nadabo hakimin Kankara, dan Iya Labarana kanen Kanwa Nuhu. Amma a cikin 1957 sai aka yi masa canjin wurin zama zuwa Bakori inda mahaifinsa ya yi sarauta.
To sai aka kawo kanensa kuma, Alhaji Muntari Nadabo a shekarar ya zama sabon hakimi. Cikin 1970 aka dakatar da shi, sannan aka kai Wakili. Wanda aka kai shi ne Sarkin Bai Alhaji Isyaku. Ya yi zama na shekara biyu, zuwa 1972.
A 1972 sai aka nada Alhaji Muhammadu Lawal, wanda shi kuma dan Madawakin Zangon Zabaro Umaru ne, kanen Kanwa Nuhu. Alhaji Muhammadu Lawal ya dade a bisa mulki, domin ya shekara 45 yana hakimcin Kankara. Ya rasu ran juma’a 17/3/2017.
To sai aka nada dan sa Alhaji Yusuf Lawal a wannan shekara, wanda shi kuma ya yi mulki na tsawon shekaru hudu (4).
To kuma sai, sabili da wasu dalilai masarautar Katsina ta dakatar da shi. A halin yanzu an nada Alhaji Ado Bello Mabai a matsayin sabon hakimi.
Mai shari’a Ado Bello, shi ne da na biyu a jerin ‘yayan Malam Bello, Maigari ko Dagacin Mabai, daya daga cikin manyan ‘yayan Sarkin Pauwa Nuhu.
Idan ba za a manta ba, Malam Bello, Allah Ya yi masa rasuwa a yayin da yake halartar aikin haji a kasa mai tsarki a cikin shekara ta 1977.
An haifi mai shari’a Ado Bello Mabai a ran 31/12/1948. Ya yi aikin lauya har ya kusan kure mizani a wannan layin. Ya yi ritaya ba da jimawa ba.
LIKE & FOLLOW US ON FACEBOOK & TWITTER