Kungiyar Buhari Nakowa (Buhari For All) Ta Tallafawa Kimanin Jama’a 1172 A Garin Kankara Jihar Katsina.
Kungiyar Buhari For All karkashin jahorancin Shugaban ta karkashin Alhaji Bello Bello Gimba Kankara ta rabawa al’ummar Karamar Hukumar Kankara da jihar Katsina da ruruwan buhannan shinkafa ga Mutane
Haka zalika kungiyar ta tallafawa Mutane 134 da buhunnan dawa domin rage radadin damuwa.
Yayin jawabin shugaban kungiyar Buhari Nakowa reshen Kankara Alhaji Bello Bello Gimba yayi bayyana wannan tallafi cewa yitone daga Kungiyar Buhari For All domin tallafawa al’ummar da tashin hankalin ‘yan bindiga ya rabosu da gidajen su domin kawar masu sa radadi da Kuma mata da maza gajiyayyu awannan yanki.
Acigaba da zantawar wakilin jaridar mu jagoran Shirin bayar da tallafin Bello Bello yayi jawabin yadda tsarin raba buhunnan yake kamar haka buhunnan shinkafa 500 an rabasu ne Mata masu marayu 500,
Mata da maza kuma buhunna 672 inda aka Rabawa mata da maza buhunna 132 na dawa.
Alhaji Bello Kuma Kara dacewa sunyi amfani da tsarin masarautun hakimai biyune dake Karamar Hukumar ta Kankara da kuma Magadddan da Suka kunsa.
Da wakilin mu ya zagaya farfajiyar da ake gudanar da wannan rabon Kayayyakin don ganema idonshi yadda ake aikin rabon ya gane inda yace yaga kowane magajin gari yaraba buhunan shinkafar bashi nan take Kamar yanda aka tsaraa ta hanyar kiran Sunayen Mutanen nasu.
Daya daga cikin masu garin da suka amfana da wannan tallafi Wanda yasamu wakilcin Bello Ahmed Rufa’i ya shaidawa wakilin namu dacewa sunyi matukar farin ciki gamida godiya wannan tallafi musanman awannan lokaci na Azumi, yakuyi Addu’a Allah ta Kara wannan yanki namu zaman lafiya da kwanciyar Hankali.
Bugu da Kari wasu daga cikin matan dasuka amfana amma suka nemi kada a bayyana subayensu sun godiya ga Allah da jagoran Shirin Buhari For All na shiyyar Kankara Alhaji Bello Bello Gimba Kankara bisa tsarin dayayi arabon kayan don tabbatar da isar kayan ga Waɗanda aka shirya dominsu.
Taron ya samu halartar Manyan Al’umma dasuka hada wakilin Karamar hukumar Kankara, Wakilan hikiman Karamar Hukumar Kankara,Sarkin Pauwan Katsina hakimin Kankara, Kanwan Katsina Hakimin Ketare,dukkanin magadddai da Mayan limaman yakunnan Kankara, Wakilan’Yan Majilisar Wakilan dana majilasar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Kankara.
Angunar da taron rabon lafiya .