Daga. Abdullahi Alhassan
A wani ya nayi na Karfafa halaga Mai dorewa tsakanin bagaren yan majalissa dana Bangaren zartarwa don cigaban Jahar Bauchi , Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad,Ya gaiyaci Yan Majalissar dokokin Jahar don bude bakin azumin watan Ramadana a fadaar Gwamnatin jahar,
da yake jawabi a lokacin bude bakin Kakakin Majalissar dokokin Jahar Bauchi ,Honarabul Abubakar Y Sulaiman , ya gode wa Gwamnan da wan nan Karamci na girmama su wanda yace hakan zai karfafa dangon zumunci tsakanin su da Gwamnatin Jahar don ciyar da jahar gaba,
Honarabul Abubakar , ya nuna godiyar sa amadadin yan Majalisar ta 9 ga Gwamnan dan basu kulawa ta musamman da yakeyi ganin yarda yake biyan su albashinsu dama sauran hakkokinsu akan kari ,dama sauran bukatun su yau da kullun,
Yayin kuma da yabawa Gwamnan kan aiyukan da yake cigaba da gudanarwa a fadin Jahar,in da ya bukace shi da ya gyara Ginin Majalisar dokokin jahar,
ganin cewa ginin ya jima tun shekara ta 1977 da aka yi shi,
Ya kuma cigaba da cewa”Mai girma Gwamna muna ganin sauran Gine-ginan Majalisssu a fadin kasar nan ,inda zakaga gini ne na zamani da kuma kayan zamani wanda hakan zai rage jinkiri wurin gudanar da aikin mu, lna rokonka da ka gyara mana, kuma nasan zaka gyara mana , zai sa muriga gudanar da aikin mu cikin kyakkyawa yanayi .
Abu na biyu,”wadan sun mu suna zama ne a wurare wani iri gaskiya wanda basu da cikekken tsaro da kuma suna lya fadawa ko wani irin hadari, nasan kayi niyar gina gidaje na falan Gwamnati uku , to a gaggauta da kuma fadada aikin da muma yan majalisa mu samu,
Wasu daga cikin yan majalisar da suka tofa albarkacin bakin su yabawa Shugabancin Kakakin Majalisar sukayi tare kuma da yabawa Gwamnan don wan nan Gaiyatar su da yayi don bude bayi dashi.
Da yake Nashi jawabin Gwamnan Jahar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, gode wa yan majalisar ya yo kan goyan baya da suke bawa Gwamnatin sa inda ya dora cigaban kan yan majalisar na bash duk goyan bayan da ya samu nasarori akan kwazun da suke nunawa don ciyar da jihar gaba.
Ya cigaba da cewa da farko an dauka cewa za’a ringa samun tashin tashina tsakanina da yan majalisar jahar nan ganin cewa yan jam’iyar adawa ne suka cikata ta APC ,sai Allah yasa da Shugabanin da sauran yan majalisar jahar ce suka sa gabansu , to sai gashi kuma babu ,saboda sa bukatun ganin majalissar jahar suka sa agabansu don yiwa jama’a aiki da kuma sauke nauyin da aka daura musu don ciyar da jahar gaba,
Lalle wan nan abun koyi ne da yakamata sauran Jahohi sukoya , shi yasa zakaga ana kirana daga wasu jahohi a kasar nan cewa wai menene sirrin ne?
Wasu ma zakaga jam’iyarsu daya da Gwamnan su amma suna samun matsala a tsakanin us.
To wan nan fa yin Allah ne kawai, saboda haka na gode muku, kuma lna kiran ku da kuguji yan cece kuce, da zasu kawo muku maganganu mutane nima haka nakeyi shi yasa kuke ganin na zauna lafiya , saboda haka muyi watsi da bambance- bambance ,kuma muyi wa kowa adalci.
Duk da karancin Kudi da jahar ke fama dashi , munyi kokarin tattara kudin shiga tare kuma da toshe kafafen da za’a riga samun sulawawar kudin jahar daga asusunta, to yanzu zamu dokufa ne wurin samar wa Jama’a aikin yi don karfafa su tare kuma da Aiwatar da aiyukan raya kasa a kowani yanki don ciyar da jahar gaba, batare da nuna bambamcin jam’iya ba,
Saboda haka yan mazabu zasu riga girma ma wanda suke wakiltar su,
Daga karshe ya yi addu’ar kasancewar ko wan nen su a babban matsayi nan gaba.