Daga Abdullahi Alhassan Kaduna.
Tsohon Ministan Matasa da wasanni a Najeriya, Barista Solomon Dalung, Yace Najeriya na Mutukar bukatar Addua- kan halin da ta Shiga na matsanancin matsalar tsaro a halin yanzu inda ya baiyana cewa a akwai bukatar Malaman addini da su himmatu wuri yiwa kasar Addu’a ganin cewa sun dage da addu’a lura da yarda ake Samun cigaba da yawaitar hare haren yan bindiga da ke wanzuwa a halin yanzu inda ake Samun asarar rayuka tare da dukiyoyi da dinbun kudade ,
Ya roki Babban Malamin kasancewar sa na Dattijo da kuma zama Mai Shekaru da yawa Wanda yaga jiya Kuma yaga yau da kuma fahim ganin gobe shikin koshin lafiya, lna kara rokon ka da sabaki ganin yarda Kasa nan ta zama haka akwai bukatar Kari ga fallan Gwamnatoci Uku da muke dasu na daukar amanar kare Rayukan Jama’a da Dukiyoyinsu,
Solomon Dalung ya baiyana haka ne yayin Ziyarar da ya kaiwa Babban Malamin addinin Musulunci a Kaduna tare da rakiyar Tauwagar Fastoci karkashin Jogorancin Sanannnen Malamin Addinin Kiristan nan dake Kaduna Fasto Yuhana Buru Wanda har ila yau shine Shugaban Kungiyar Farfado da Sasanta Jama’a , da Malaman addini Musulunci da Kungiyoyin Matasa da na cigaban Al’umma da Tauwagar Manema labarai daga Kafafen yada labarai daban- daban na cikin Gida da wajen Kasar nan, don Bude bakin / iftar dashi ,na Azumin watan Ramadana da ake cigaba dayi a halin yanzu,
Shi kuwa a nashi Jawabin ,Sanannnen Malamin Addinin Musuluncin Sheikh Dahiru Usman Bauchi ,cewa yayi “bazamu mance da Alherin da Kiristoci sukayi Mana ba,na bawa Musulmi kariya yayin da Mushirikan Makkah suke ta azabtar da su,wan nan yasa Annabi Muhammad (S W A)ya tura su wurin Sarki Habasha na wacen lokacin Najashi wanda shi Kirista ne Kuma Mai adalci don ya basu kariya na rayukansu tare kuma da ganin an Kyautata musu a Chen,
Ya Kuma cigaba da cewa Addinin Kirista
Addinin Tausayine shi kuma Addinin Musulunci Addinin Zaman lafiya ne, to meya kawo rikici tsakanin mai addinin zaman lafiya da kuma mai addinin Tausayi ne? Inda wanda Musulmi sukafi kusanci da shi shine Addinin Kirista ,to Muna godiya da wan nan Zumunci na kusan Shekaru goma da wan nan Tauwagar kan kawo mini duk Shekara ,
Inda yayi Addu’ar Samun zaman lafiya a Najeriya tare kuma da kira da Gwamnati Uku da su cika alkawuran da suka dau ka nauyin kare Rayukan Jama’a da kuma Dukiyoyinsu tare kuma da Addu’ar Sake dawo da dauwamen – men zaman lafiya a Najeriya baki daya.