Mazauna set light area 4 a rigasa, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna ranar Juma’a 23 ga watan Maris 2021 sun tashi da wani mummunan lamarin, yayinda wasu mugayen mutane da ba a san su ba suka kashe wani karamin yaro wanda har yanzu ba a gano shi ba.
Yaron mai shekaru tsakanin 12 zuwa 15 ya kone ta yadda ba za a iya gane shi ba a cikin wani gini da ba a kammala ba.
Mazauna yankin sun bayyana matukar kaduwarsu da kuma nuna bacin ransu game da rashin kyakkyawan tsaro a yankin.
https://www.youtube.com/watch?v=C96eieCswd0
An gano gawar ne lokacin da wasu kananan yara suka shiga ginin da ba a kammala ba suna wasa, sai suka ga gawar suka kira dan uwansu Isiyaku Salisu.

Bayan na ga gawar, sai na umarci yaran da su kira Mai Anguwa don sanar da shi irin munanan abubuwan da suka faru, Isiyaku Salisu ya kara da cewa.
Mai Anguwa, Aliyu Baushe ya tabbatarwa Jaridar Daily Episode faruwar lamarin yayin da yake bayyana kaduwarsa, ya yi addu’ar Allah ya tona asirin wadanda ke wannan aika-aika.
Da na isa wurin, na hanzarta sanar da jami’an tsaro na yankin da kuma masarautar wadanda suka umurce ni da in kira ‘yan sanda, in ji Mai Anguwa.