Majalisar dattijan Najeriya ta nemi gwamnonin jihohin kasar 36 su bai wa bangaren shari’a damar cin gashin kai,ba tare da wata sasantawa ba.
Opeyemi Bamidele wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar na bangaren shari’a, ‘yancin dan adam da harkokin shari’a, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Kungiyar ta tsunduma yajin aiki a baya-bayan nan tare da shirya zanga-zanga kan gazawar gwamnati na tabbatar da ‘yancin cin gashin kan bangaren shari’a.
Bamidele ya ce akwai bukatar a bai wa bangaren shari’a yanci domin tabbatar da dimokradiyya a Najeriya, yana cewa in an tabbatar da hakan babu wanda zai ragu da komai.
“Babu wanda zai ragu da wani abu in aka tabbatar da mana da ‘yancin cin gashin kai a matakin jihohi, tun da an yi a matakin kasa,” in ji shi.
“Muna neman gwamnonin jihohi sun tabbatar da wannan ‘yanci saboda ‘yancin bangaren shari’a ba abu ba ne da za a tsaya ana sasantawa a kai.