Labarin zargin Ministan Sadarwanda Dr Isah Ali Pantami kasancewa cikin jerin mutunen da Amurke ke nema saboda daukar nauyin ta’addanci, ya tayar da kura matuka. Daga bisani ya bayyana cewa labarin ba shi da tushe.
Binciken Aminiya ya gano cewa babu ko da kalmar Pantami, ballantana wani mutum mai suna Isa Ali, ko Isa Ibrahim, a cikin jerin mutum 45 da hukumomar tsaro ta FBI ta Amurka take nema ruwa a jallo kan zargin ayyukan ta’addanci a cikin kasar ko a kasashen duniya.
Kafar intanet ta Independent da ta wallafa labarin da ya bayyana cewa shaci-fadi ne, ta ambato wani hadimin Pantami -wanda ba ta bayyana sunansa ba- yana karyata rahoton a matsayin labarin kanzon kurege.
”Wannan yunkuri ne kawai na cin mutunci da kuma cin zarafin addinin da akidar mutum. Gwamnatin Amurka ba ta zargin sa da komai,” inji hadimin Ministan cikin bacin rai ga Independent da ta wallafa labarin karyar.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito kakakin Ministan, Misis Uwa Suleiman, ta tana cewa, “an buga labarin ne da zummar ɓata sunan ministan.
“Ta ce wasu mutane ne da suka rasa yadda za su bullo wa Pantami domin su muzanta shi – shi ne suka fake da ƙirƙirar labarin.”
Bayanan na zuwa ne bayan labarin da wasu kananan kafafen shafukan labaran intanet a Najeriya suka wallafa cewa Amurka ta sanya sunan Pantami a cikin jerin mutanen da take zargi da daukar nauyin ayyukan ta’addanci, saboda akidar Salafiyya da yake bi.
Kafin nada shi matsayin Minista, Pantami ya kasance shahararren mai wa’azin Musulunci.
Hakan, a cewar labarin da karyarta ne Indepent, ya sa Amurka ke zargin ra’ayoyinsa na da alaka da kungiyar Al-Qaeda kuma yana da kusanci da da tsohon Shugaban Boko Haram wanda jami’an tsaro suka kashe, Mohammed Yusuf.
Sai dai kuma tuni hadiman Ministan suka karyata rahoton a matsayin kanzon kurege.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER