Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, yana mai cewa “duk wani yunkuri na haramtacciyar hanya don hambarar da gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokiradiyya ba abin kyama ba ne kawai, har ma gwamnatocin dimokuradiyya a duniya ba za su amince da shi ba.”
Da yake magana a tattaunawa ta wayar tarho da Mahamadou Issoufou, takwaransa kuma Shugaban mai barin gado kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar, Shugaba Buhari ya yi gargadin cewa “kasashen duniya na adawa da canjin gwamnati ta hanyar amfani da karfi da kuma hanyar da ba ta dace da tsarin mulki ba.”
“Hankalin banza ne kawai a yi kokarin cire zababbiyar gwamnati da karfi.
“Ya kamata masu son siyasantar da sojoji su mutunta muradin mutane tare da mutunta tsarin mulki.
“Na damu musamman game da mummunan tasirin juyin mulki ga kwanciyar hankalin Afirka, zaman lafiya da ci gaba.
“Najeriya ba za ta nuna halin ko-in-kula ba game da wadannan hadurran ga Afirka. Juyin mulkin ba shi da kyau kuma shigar sojoji cikin mummunan canjin gwamnati na cutar da Afirka fiye da alheri”, in ji Shugaban.
Shugaban na Najeriya ya bukaci shugabannin Afirka da su “kasance a dunkule wajen yaki da juyin mulki ta kowace irin hanya,” yana mai gargadin masu yunkurin juyin mulkin da su dauki darasi daga tarihi kan illar rashin zaman lafiya da ke faruwa sakamakon mummunar mamayar gwamnatoci.
Shugaba Buhari ya kuma yi amfani da wannan damar wajen taya zababben Shugaban kasar Mohamed Bazoum murnar nasarar zaben da kuma sadaukarwar Shugaban mai barin gado na mika mulki cikin tsari da lumana.
Shugaban na Najeriya ya kuma jinjina wa jami’an tsaron Nijar saboda murkushe hare-haren da ake kaiwa ga zababbiyar Gwamnatin dimokiradiyya ta mutanen Jamhuriyar Nijar.
Garba Shehu
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa
(Kafofin watsa labarai & Jama’a)
Maris 31, 2021