Rahotanni sun bayyana cewa rashin kyawun yanayi ya hana Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo halartar bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmad Tinubu a Kano.
Bayan Osinbajo, kakakin majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal dana wakilai, Femi Gbajabiamila da Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da dai sauransu na daga wanda gurbatar yanayin yawa cikas wajan halartar wannan biki.
Saidai kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande ya bayyana cewa, Osinbajo zai halarci zaman ta kafar sadarwar zamani.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER