Wata babbar kotu a jihar Akwa Ibom ta yanke wa Peter Ogban, farfesa a fannin kimiyyar kasa a jami’ar Calabar, shekaru uku a gidan yari saboda murde sakamakon zabe.
Ogban shi ne jami’in tattara sakamakon zaben sanata a Akwa Ibom arewa maso yamma a 2019.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ce ta gurfanar da shi.
Kotun ta same shi da laifin sauya sakamakon zaben don fifita jam’iyyar All Progressives Congress (APC) akan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).