Gobara na ci gaba da ci a Babbar Kasuwar garin Katsina, Jihar Katsina.
Gobarar wacce ke ci tun da safiyar Litinin ta jawo asarar dukiyoyi na miliyoyin Nairori.
Zuwa yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, kusan ilahirin shagunan da ke bayan bankin Unity da ke cikin kasuwar sun kone kurmus kamar yadda Aminiya ta ruwaito.


Har zuwa hada wannan rahoton dai ma’aikatan kwana-kwana na ci gaba da kokarin kashe wutar da wasu majiyoyi ke cewa ta tashi ne a bangaren masu injin nika da kayan abinci.

DAILY EPISODE HAUSA
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER