Rahotanni daga Jihar Borno sun bayyana cewa wani mutum mai shekara 50 da aka bayyana sunansa da Modu Isa ya yi yunƙurin kashe kansa bayan matar da ya saki taki amincewa ta dawo gidansa.
Wakilinmu ya tattaro cewa lamarin ya faru ne a unguwar Hausari da ke ƙaramar hukumar Bama, inda mutumin ya yi wa kansa mummunan rauni ta hanyar caka wuƙa sau da dama tare da yanke al’aurarsa.
Majiyoyi sun bayyana cewa tsohuwar matarsa, Bayanex Modu, ta ƙi komawa gidansa ne saboda a baya ya sake ta har sau uku, wanda a shari’ar Musulunci bai da damar hakan ba.
An garzaya da wanda abin ya faru da shi zuwa Asibitin Gwamnati na Bama, inda yake samun kulawa a yanzu bayan raunukan da ya samu.
Haka kuma, rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan yadda abin ya faru.
KU BIYO MU A FACEBOOK