Kasa da sa’o’i 24 da haihuwarsa, jariri mai suna Salisu Sale wanda aka haifa da cutar gastroschisis – wata larura da ake haihuwar jariri da kayan cikinsa a waje, dukda kasancewar ana buktar yimasa aiki cikin gaggawa, anma hakan bata samu ba sakamakon likitoci na yajin aikina asibitocin gwamnati a fadin ƙasar nan.
Jaririn, wanda aka haifa a unguwar Dakido, da ke ƙaramar hukumar Malam Madori ta jihar Jigawa, an garzaya da shi zuwa Asibitin Gwamnati na Hadejia da sassafe a ranar Talata, 29 ga Yuli, amma ba a samu damar yi masa aiki ba sabida ƙarancin kayan aiki da rashin kayan aikin tiyata, kamar yadda mahaifinsa, Malam Sale, ya shaidawa Daily Episode.
A cewarsa:
“An tura mu zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), muka isa da gaggawa, amma abin takaici, likitoci na yajin aiki ne – ba a duba jaririna ba.”
“Daga bisani, aka shawarce mu da mu tuntubi wani gidauniyar taimako, USN Cares Foundation, da ka iya tallafa mana, domin ba mu da halin biyan kudin tiyata a asibitin masu zaman kansu.”
“Duk da haka, muna addu’a Allah Ya kawo sauƙi, domin jaririna ya rayu,” in ji shi.
Shugabar USN Cares Foundation, Ummusalma Nasir, ta bayyana halin da jaririn ke ciki, inda ta roƙi jama’a da su taimaka:
“A halin yanzu, ba’a samu damar yima jaririn tiyata ba. Mun garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa mai suna Soft Care a Kano, amma muna buƙatar biyan kuɗi kafin a fara jinya.
Muna roƙon jama’a su taimaka da gudummawa domin ceton rayuwarsa.”
Domin Taimako: 📞 Lamba: 08039654603
🏦 Asusun Banki: Lambar Asusu: 1220898114, Banki: Zenith Bank Sunan Asusu: USN Cares Foundation
KU BIYO MU A FACEBOOK