Biyo bayan hasashen da Hukumar Yanayi ta Ƙasa (NiMet) da Hukumar Kula da Ruwa ta Ƙasa (NIHSA) suka fitar, wanda ke nuna cewa wasu al’ummomi a sassa daban-daban na ƙasar na fuskantar barazanar ambaliya, manajan Dam ɗin Tiga, Alhaji Abdulkadir Salisu, ya yi kira ga manoma da mazauna yankunan da ambaliya ke yawan afkuwa da su bi matakan kariya tare da shiryawa domin ficewa daga yankunan kafin lokaci ya kure.
A wata tattaunawa da Jaridar Daily Episode, Salisu ya karyata zargin cewa ambaliyar da ta mamaye wasu kauyuka a Kano da Jigawa sakamakon sakin ruwa ne daga Dam ɗin Tiga.
A cewarsa:
“Wannan ambaliya da mutane ke fuskanta a halin yanzu ruwa ne daga ruwan sama mai karfi — ba daga Dam ɗin Tiga ba. Saboda dam din Tiga yakan fara sakin ruwa ne daga watan Agusta zuwa Satumba.”
Ya kara da cewa akwai tsarin da suka tanada wanda ke bai wa jama’a, musamman shugabannin al’umma kamar hakimai da dagatai, bayani game da matakin ruwa a Dam, domin a shirya tun kafin matsala ta faru.
“Wasu mutane suna komawa gidajensu da wuri bayan ruwa ya lafa, alhali hakan ba daidai ba ne. Yakamata a bar yankunan da ambaliya ke barazana tuni, domin ruwan sama na kara taruwa a rafuka da koguna, wanda ke haddasa kwararar ruwa cikin al’umma da ke jawo ruɗani cewa dak Dam ne ake sakin ruwan.”
Alhaji Salisu ya bukaci mazauna yankunan kogin da sauran wuraren da aka san suna fuskantar ambaliya da su fara shirin ficewa tun yanzu, duba da cewa watan Agusta na ƙaratowa.
“Ko da yake ba za mu iya dakatar da abubuwan da suka shafi halitta ba, musamman ma idan sun faru cikin dare, amma matakan kariya sun fi muhimmanci. Yakamata kowa da kowa da ke zaune a kusa da koguna ya dauki matakin gaggawa kafin abin ya lalace.”
KU BIYO MU A FACEBOOK