Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa ba za ta zaunawa da shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, domin tattaunawar sulhu ba, har sai ya dauki matakai na ainihi da suka hada da dakatar da hare-hare da sakin mutanen da ke hannunsa.
Kanar Ahmed Usman (mai ritaya), wanda shi ne mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, biyo bayan bayyanar wani faifan bidiyo da Bello Turji ya fitar, inda ya bukaci a shiga tattaunawa da shi.
Turji dai wanda aka dade ana zarginsa da jagorantar munanan hare-hare a Sakkwato da wasu jihohin makwabta, ya saki bidiyon ne kwanaki bayan jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin manyan kwamandojinsa sama da dari, a hadin gwiwa da jami’an tsaro na kasashen waje ciki har da Faransa.
Kanar Ahmed ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da cewa bukatar sulhun Bello Turji na gaskiya ne, sai dai idan ya saki duk mutanen da ke tsare a hannunsa tare da dakatar da kai farmaki a yankunan da ke fama da rikice-rikice.
“In har yana da niyyar zaman lafiya da gaskiya, to dole ne ya daina kai hare-hare a kauyuka da saki wadanda ya yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba,” in ji Kanar Ahmed.
Ya kara da cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunkuri na tattaunawa yayin da jama’a ke rayuwa cikin fargaba, kuma ‘yan bindiga na ci gaba da addabar su.
A cewarsa, “Zaman lafiya na bukatar matakan gina amana daga bangarorin da abin ya shafa, ba kawai kalmomi ba.”
Kanar Ahmed ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar samar da tsaro da kwanciyar hankali, kuma ba za ta lamunci ta’addanci da sauran laifuka ba.
A karshe, ya bukaci hadin kan al’umma, shugabannin gargajiya, malamai da kungiyoyin fararen hula wajen marawa gwamnati baya domin dorewar zaman lafiya a jihar.
KU BIYO MU A FACEBOOK