">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Wednesday, October 15, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Dalilan Da Suka Tilasta Ganduje Murabus Daga Shugabancin Jam’iyyar APC 

by Abubakar Ismail kankara
June 28, 2025
in Labarai
0
Ganduje
Share on FacebookShare on Twitter
">

Rahotanni sun bayyana dalilan da suka tilasta wa shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, murabus daga mukaminsa a ranar Juma’a.

An nada Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar a ranar 3 ga Agusta, 2023, bayan da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu, ya yi murabus da tilas daga mukamin.

Jaridar DAILY NIGERIAN ce ta fara bayyana labarin murabus dinsa, inda ta ambato matsin lamba daga yankin Arewa ta Tsakiya a matsayin daya daga cikin dalilan da suka kawo karshen shugabancinsa da gaggawa.

Sai dai majiyoyi da ke da masaniya game da batun sun bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne da kansa ya umarci Ganduje da ya yi murabus, bayan da hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ta mika masa rahoto da ke zargin Ganduje da aikata cin hanci da rashawa.

RelatedPosts

Daga Aikatau Zuwa Mallakar Filaye: ‘Matan da ke Alfahari da Sauyin da Suka Samu’

Yan sanda a Kano Sun Gurfanar da Mutane 333 Da Aka Kama Lokacin Zaben Cike Gurbi a Kotu

Yadda Aka Gudanar da Aikin Gyaran Makabarta a Dala

Wani Magidanci Yayi Yunƙurin Kashe Kansa Tare da Yanke Al’aurarsa Sabida Matar Daya Saka Taki Amincewa Ta Dawo

Rikici a Zaben Mazabu Ya Kara Dagula Lamura

Wani muhimmin abu da ya kara tsananta matsin lamba a kan Ganduje shi ne yadda aka gudanar da zabukan fidda gwani a kananan hukumomin babban birnin tarayya, musamman a karamar hukumar Bwari, inda ake zargin an canza sakamakon zabe a bisa biyan kudi.

Wani mai lura da yadda aka gudanar da zabukan Bwari, Enyigwe Matthew, ya wallafa a shafin sada zumunta cewa:

“Zaben fidda gwani na APC da na halarta a Liberty Hotel a Bwari ya nuna min cewa Ganduje ba zai dade ba a shugabancin jam’iyyar. Tun da aka kawo jerin sunayen wakilai, sai aka kori ‘yan takara da ‘yan jarida da taimakon ‘yan sanda.”

Umurni Daga Fadar Shugaban Kasa

Majiyar tsaro ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa shugaban kasa ya umurci SSS da su gudanar da bincike kan zargin karbar cin hanci a lokacin zabukan.

Bayan mika rahoton binciken, shugaban kasa ya gayyaci shugaban kungiyar gwamnonin APC, Gwamna Hope Uzodinma na Imo da mai taimaka masa kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, inda ya bukace su da su shawarci tsohon gwamnan kanon da ya yi murabus da mutunci.

Daga bisani Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya hada kansa da su wajen isar da sakon shugaban kasa ga Ganduje.

Ganduje Ya Yi Kokarin Tsaida Murabus Din

A daren Alhamis, Ganduje ya yi yunkurin ganin shugaban kasa don rokon a bar shi ya jagoranci jam’iyya har zuwa taron gangami na watan Disamba 2025.

Amma da safiyar Juma’a, bayan ganawa da shugaban hukumar SSS, Adeola Ajayi, Ganduje ya mika takardar murabus dinsa, inda ya ce yana fama da matsalar lafiya — amma majiyoyi sun tabbatar da cewa wannan kawai wata hanya ce ta fuska.

Yunkurin Da Ya Gabata Na Tsige Ganduje

Tuni dai shugaban kasa ya taba yunkurin cire Ganduje saboda korafe-korafe daga yankin Arewa ta Tsakiya kan rashin daidaito da kuma zargin cin hanci da rikon kai.

A watan Agusta 2024, an yi niyyar mayar da Ganduje jakadan Najeriya a wata kasa ta Yammacin Afirka. Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne aka umurta da isar da sako gare shi.

Sai dai Ganduje ya je ya nemi goyon bayan tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Bisi Akande, wanda ya roki Tinubu da ya bari Ganduje ya ci gaba da jagoranci jam’iyya zuwa Disamba 2025.

Rikici Da Tsoffin Abokan Siyasa

Matsalar Ganduje ta kara kamari bayan rikici da tsoffin abokan siyasa biyu masu karfi: Gwamna Hope Uzodinma na Imo da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Ganduje ya shiga harkokin APC na Kudu Maso Gabas ba tare da tuntuba ba, musamman batun zaben gwamna a Anambra. Haka kuma ya juya baya ga Akume a rikicin APC na Jihar Benue, inda ya goyi bayan Gwamna Hyacinth Alia, duk da wata yarjejeniya da ya yi da Akume.

Zarge-Zargen Cin Hanci

A shekarar 2018, jaridar DAILY NIGERIAN ta fitar da faifan bidiyo da ke nuna Ganduje yana karbar dalolin cin hanci daga hannun wani kwangila, wanda hakan ya haifar da bincike a majalisar dokokin jihar Kano.

Yanzu haka Ganduje, tare da matarsa da dansa, na fuskantar shari’a kan zargin karkatar da kudade da suka kai sama da biliyan N50 a jihar Kano.

">
">

DAILY EPISODE HAUSA

KU BIYO MU A FACEBOOK

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

Daga Aikatau Zuwa Mallakar Filaye: ‘Matan da ke Alfahari da Sauyin da Suka Samu’

Daga Aikatau Zuwa Mallakar Filaye: ‘Matan da ke Alfahari da Sauyin da Suka Samu’

by Yahuza Bawage
October 6, 2025
0

A wasu yankuna da ke kudancin jihar Kaduna a arewacin Najeriya, mallakar fili, musamman na noma, wani abu ne da...

zaben cike gurbi

Yan sanda a Kano Sun Gurfanar da Mutane 333 Da Aka Kama Lokacin Zaben Cike Gurbi a Kotu

by Abubakar Ismail kankara
August 18, 2025
0

Tun bayan kammala zaben cike gurbi da aka gudanar a fadin kasar nan, rundunar yan sandan jahar ta bayyana irin...

Yadda Aka Gudanar da Aikin Gyaran Makabarta a Dala

Yadda Aka Gudanar da Aikin Gyaran Makabarta a Dala

by Abubakar Ismail kankara
August 18, 2025
0

Duba da yadda rashin magudadan ruwa ke sanadiyar rubtawar kabaruruka musamman a lokutan damina, al’ummar unguwar Dala da kewaye dake...

yunƙurin kashe kansa

Wani Magidanci Yayi Yunƙurin Kashe Kansa Tare da Yanke Al’aurarsa Sabida Matar Daya Saka Taki Amincewa Ta Dawo

by Abubakar Ismail kankara
August 17, 2025
0

Rahotanni daga Jihar Borno sun bayyana cewa wani mutum mai shekara 50 da aka bayyana sunansa da Modu Isa ya...

Sarkin Rano Ya Haramtawa Iyaye Aurar da ’Ya’ya Mata Kafin Kammala Makarantar Firamare

Sarkin Rano Ya Haramtawa Iyaye Aurar da ’Ya’ya Mata Kafin Kammala Makarantar Firamare

by Abubakar Ismail kankara
August 16, 2025
0

A dai-dai lokacin da ake fama da yawan yaran da basa zuwa makaranta musamman a fadin arewacin kasar nan, mai...

Tsaro Ya Inganta

Kasa da Awa Ɗaya Bayan Ya Wallafa Cewa Tsaro Ya Inganta, ’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shi

by Abubakar Ismail kankara
August 15, 2025
0

Rahotan da Daily Episode Hausa ta tattara daka jaridar idon mikiya na nuna da cewa, yan bindiga dake yawan kashe...

Next Post
Marigayi Alhaji Aminu Dantata

Gwamnatin Saudiyya Ta Amince a  Binne Marigayi Alhaji Aminu Dantata a Madina

yan bindiga

Ba Zaman Sulhu Idan Har Kana Ci Gaba da Ta’addanci — Gwamnatin Sakkwato Ga Bello Turji

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In