Wata kotun Shari’a da ke zama a Magajin Gari, Jihar Kaduna, ta yanke wa wani matashi mai suna Yusuf Usman hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa laifin satar takalman masallata a masallacin Government College.
Usman ya amsa laifukan kutsen haramtacciyar hanya da sata, inda alkalin kotun, Malam Kabir Muhammad, ya yanke masa hukunci a ranar Talata. Duk da haka, alkalin ya ba shi zabin biyan tarar naira dubu biyar (₦5,000) maimakon zaman gidan yari.
Bayan haka, kotun ta umarci Usman da ya biya naira dubu dari da hamsin (₦150,000) a matsayin diyya ga kwamitin masallacin. Alkalin ya gargade shi cewa rashin biyan wannan kudin diyya zai kai shi ga kara shafe shekara guda a gidan yari.
Tun da farko, mai gabatar da kara, ASP Luka Sadau, ya bayyana wa kotu cewa an kama wanda ake zargi ne a ranar 13 ga Yuni, bayan da membobin kwamitin masallacin suka damke shi suka mika shi ga ‘yan sanda.
A cewar Sadau, “Bayan sallar Jumma’a, wanda ake zargin ya saci takalma na darajar naira dubu dari (₦100,000) mallakin wasu masallata. A lokacin bincike, ya amsa cewa yana yawan zuwa masallaci a ranakun Jumma’a domin satar takalma, wanda daga bisani yake kaiwa kasuwar Litinin ko Maraban Rido domin sayarwa.”
KU BIYO MU A FACEBOOK