Masarautar Gaya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta sanar da cire Alhaji Usman Alhaji daga mukaminsa na Wazirin Gaya.
Wannan mataki na masarautar ya fito ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar, Munzali Muhammad Hausawa, ya fitar a yammacin Laraba, inda aka bukaci jama’a da su dauki batun da muhimmanci tare da yin abin da ya dace.
A cewar wata wasika da aka tura wa Alhaji Usman Alhaji, wanda kuma ya taba rike mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano a zamanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, masarautar ta bayyana cewa ta janye sarautar ne saboda wasu dalilai masu muhimmanci da ba za a iya watsar da su ba, kuma saukar ta fara aiki nan take.
Sakataren Masarautar Gaya, Alhaji Bello Halilu, ya bayyana godiyar masarautar ga Alhaji Usman Alhaji bisa irin gudunmawar da ya bayar lokacin da yake rike da mukamin Wazirin Gaya, musamman wajen tallafawa harkokin masarauta da ci gaban al’adu da tarihi.
Sanarwar ta kara da cewa wannan sauyi wani bangare ne na kokarin masarautar wajen kare mutunci da martabar sarauta da kuma tabbatar da daidaito da al’adun gargajiya da suka ginu bisa tarihi da tsari.
KU BIYOMU A FACEBOOK