Wani magidanci mai shekaru 60 da haihuwa, Adamu Mohammed, ya kashe diyarsa Zainab Adamu mai shekaru 18 a unguwar Dawakin Dakata da ke jihar Kano, yayin wata arangama a cikin gida.
Rahoton da Zagazola Makama, wata kafar labarai da ke mayar da hankali kan matsalolin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Litinin da misalin karfe 5:00 na safe. Ana zargin mahaifin ne da dukan diyarsa da wani abu mai nauyi wanda ya bar ta cikin rashin lafiya.
Bayan kusan awa biyu da faruwar lamarin, makwabta sun fara zargin wani abu ya faru, inda suka dauki matakin gaggawa na sanar da hukumomi. ‘Yan sanda sun kai dauki zuwa gidan, kuma an garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Sir Sunusi Specialist da ke Kano.
Sai dai, likita a asibitin ya tabbatar da cewa yarinyar ta rasu sakamakon raunukan da ta samu.
An mika gawar Zainab ga iyalanta don yin jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. A halin yanzu kuma, ‘yan sanda sun kama mahaifinta kuma ana cigaba da gudanar da bincike don gano musabbabin aikata wannan aika-aika.
Wani mazaunin unguwar ya bayyana lamarin a matsayin abin firgita da takaici, inda ya ce akwai bukatar kara wayar da kan al’umma game da illar tashin hankali a cikin gida, musamman tsakanin ‘yan uwa na jini.
KU BIYO MU A FACEBOOK