A yankin Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara, an gudanar da Sallar rokon ruwan sama bayan kwanaki da dama da rashin ruwan sama ya dami al’umma. Wannan ya janyo damuwa da fargaba, musamman ganin cewa lokacin damina na kusa karewa, amma ba a sami ruwan shuka ba.
Sallar rokon ruwan saman dai ta samu halartar dimbin jama’a, ciki har da manoma da malaman addini da sauran mazauna yankin da ke cikin fargabar yadda zasu shuka da kuma samun amfanin gona a kakar bana.
Liman Malam Badamasu ne ya jagoranci Sallar, inda Sheikh Malam Muhammad daga unguwar Gangaren Makaranta ya gabatar da wa’azi mai karfi kan abubuwan da ke haddasa irin wadannan masifu da kuma muhimmancin komawa ga Allah da yawaita ibada a irin wannan lokaci.
Sheikh din ya jaddada cewa, “Rashin ruwan sama yana da nasaba da zunubai da halayenmu. Ya kamata mu gyara halayenmu, mu nemi gafara, mu kuma yawaita addu’o’i don samun rahamar Allah.”
Daga karshe, ya roki Allah da ya saukar da ruwan rahama mai albarka a yankin da ma kasa baki daya.
KU BIYO MU A FACEBOOK