Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa fiye da mutane 700 har yanzu ba a gansu ba bayan mummunar ambaliya da ta afku a karamar hukumar Mokwa na jihar.
Gwamna Umaru Bago ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi bakuncin Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon jami’in tsaron marigayi Janar Sani Abacha, da wasu abokansa da suka kai ziyarar jaje bisa ibtila’in ambaliyar da ta auku a Minna a ranar Talata.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Yakubu Garba ya wakilta, ya ce mutane 207 sun mutu, kana gidaje fiye da 3,000 sun lalace sakamakon iftila’in.
“Fiye da mutane 700 sun bace kuma har yanzu ba mu san inda suke ba. Ambaliyar ta haifar da barna mai yawa,” in ji Gwamna Bago.
Ya ƙara da cewa, gidaje 400 sun samu lahani, inda 283 daga ciki suka rushe gaba ɗaya, har da shaguna 50 da aka lalata.
Gwamnan ya gode wa mutane da hukumomi da suka kawo gudunmawa da agaji, yana mai cewa wannan bala’i ya shafi kasa baki ɗaya, ba jihar Neja kawai ba.
Ya ce gwamnati na aiki da masana don gano musabbabin ambaliyar, kuma ana jiran sakamakon binciken.
A nasa jawabin, Hamza Al-Mustapha ya ce sun zo ne domin yi wa gwamnatin Neja da mutanen Mokwa ta’aziyya bisa iftila’in da ya faru.
“Mun zo ne don nuna alhini bisa asarar rayuka da dukiyoyi. Muna fatan hakan ba zai kara faruwa ba,” in ji shi.
Ya ce tawagar ta kunshi manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar, kuma sun zo ne da niyyar ba da tallafi da shawarwari ga gwamnati da al’umma.
Ya bayyana cewa za su gana da majalisar gargajiya ta Mokwa, don tattaunawa kan hanyoyin da za a magance irin wannan iftila’i a nan gaba tare da inganta tsare-tsaren birane da yanayin zama.
Bayan haka, Al-Mustapha da tawagarsa sun kai ziyara ta girmamawa ga tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd.).
KU BIYO MU A FACEBOOK