Iyalan wasu mabiya darikar Tijjaniyya 13 daga Jihar Kano da aka sace a kasar Burkina Faso kimanin watanni tara da suka gabata sun sake mika kukansu ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da su dauki matakin gaggawa don kubutar da ‘yan uwansu.
Sun kuma bukaci hadin gwiwar Mai baiwa Shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu; Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II; da kuma shugabannin darikar Tijjaniyya a gida da waje, da su taimaka wajen ganin an sako wadanda aka sace din.
Rahotanni daga PRIME TIME NEWS sun nuna cewa an sace mutanen ne a watan Satumba na shekarar 2024 yayin da suke kan hanyarsu zuwa Kaolak, kasar Senegal, domin halartar babban taron darikar Tijjaniyya.
Wata daga cikin matan da mijinta ke cikin wadanda aka sace, wadda ta bayyana sunanta da Amina, ta bayyana cewa tun bayan bacewar mijinta rayuwa ta gagare ta sosai. A cewarta, tana cikin damuwa da tsananin kunci tun daga lokacin da mijinta ya bace, inda ta ce yanzu tana kokawa da ciyar da ‘ya’yanta uku.
“Duk shekara suna tafiya taron, suna dawowa lafiya. Amma wannan karon ba su dawo ba. Rayuwa ta canza, babu wanda ke kula da mu kamar da. Mutanen da suka fara taimaka mana ma sun fara gajiya,” in ji Amina cikin kunci.
Amina ta roki hukumomi su dauki mataki don ganin an sako mijinta da sauran wadanda aka sace tare da shi.
Shi ma wani dan uwan daya daga cikin mutanen da aka sace, Bashir Tijjani, ya ce tun bayan faruwar lamarin, iyalan mutanen na cikin fargaba da rashin tabbas. Ya ce duk da kokarin da suka yi, ba su samu wata kwakkwarar nasara ko bayanin inda ‘yan uwansu suke ba.
“Sun tashi daga Zawiyyar Sheikh Malam Tijjani ‘Yan Mota a Kano a ranar 7 ga Satumba, sun bi ta Jamhuriyar Nijar zuwa Burkina Faso a hanyarsu ta zuwa Senegal,” in ji Bashir. “Amma a kan iyakar Nijar da Burkina Faso ne wasu ‘yan bindiga suka tare su, suka saki mata uku daga cikin su, suka tafi da maza 13 zuwa daji.”
Ya kara da cewa sun tuntubi shugabannin Tijjaniyya a gida da waje, ciki har da Sarkin Kano, Alhaji Sanusi II, wanda ya tura wakili zuwa Damagaram domin neman bayani daga Sarkin Damagaram. Bayan wannan ganawa, an sanar da ‘yan sanda a Kano, daga bisani kuma an tura batun zuwa Abuja.
Sai dai har zuwa yanzu babu wani sahihin bayani daga bangaren gwamnati ko shugabannin darikar Tijjaniyya kan matakin da aka dauka. Bashir ya yaba da kokarin wasu daidaikun mutane kamar Alhaji Hadi Daura, wanda ya kashe kudinsa wajen kokarin ceto wadanda aka sace.
Iyayen wadanda aka sace din suna rokon gwamnati, hukumomin tsaro, da shugabannin addini da su gaggauta daukar mataki don ceto ‘yan uwansu da har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.
KU BIYO MU A FACEBOOK