Wani Farfesa a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, Farfesa Abubakar Roko, ya rasu bayan fama da rashin lafiya mai tsanani, yana jiran tallafin kudin da za a yi masa tiyata a ƙasar Masar.
Marigayin, wanda malami ne a Sashen Kimiyyar Kwamfuta, a cikin Kwalejin Kimiyya da Lissafi, na buƙatar naira miliyan 13 domin yin tiyata da zunman ceto ransa a cibiyar lafiya da ke ƙasashen waje.
A kokarin ganin an ceci rayuwarsa, Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Jami’ar ta roƙi jama’a da su bada gudummawa ta hanyar kafafen sada zumunta. Sai dai, har rai yai halinsa, ba a samu cika adadin kuɗin da ake bukata ba.
An tabbatar da rasuwar malamin ne ta shafin Facebook na ƙungiyar tsafin dalibai na jami’ar, inda suka bayyana cewa:
“Muna cikin jimami da alhini da mummunan rashin Farfesa Abubakar Roko. Ya kasance malami a Sashen Kimiyyar Kwamfuta har zuwa karshen rasuwarsa. Muna godiya ga dukkan waɗanda suka bayar da tallafi da addu’o’i a lokacin wannan ƙalubale. Allah ya saka da alheri, ya jikansa da rahama.”
Rasuwar ta haddasa martani daga al’umma a shafukan sada zumunta, inda da dama ke sukar gwamnati saboda rashin tallafi ga lafiyar malamai. Wasu na kiran a gyara fannin lafiya da walwalar ma’aikata, musamman a harkar ilimi.
Rasuwar Farfesa Roko ta sake bayyana irin gagarumin gibin da ke cikin tsarin kiwon lafiya a Najeriya, wanda ke barin jama’a cikin hali na nema da roƙon tallafi don kula da lafiyar su.
KU BIYO MU A FACEBOOK