Hukumar Kiyaye Hadurran Hanya ta Ƙasa (FRSC) ta fitar da gargadi ga direbobi da fasinjoji da ke amfani da hanyar Abuja zuwa Kaduna, musamman a gabanin bukukuwan Sallah, da su kiyaye dokokin zirga-zirga bayan da wani hadarin tanka ya haddasa cunkoson da ya katse zirga-zirga a hanyar gaba ɗaya.
Rahoton ya nuna cewa hadarin ya faru ne kimanin kilomita biyu bayan garin Jere, kusa da ƙauyen Katari, inda wata tanka ta yi hatsari a babban titin Abuja-Kaduna, wanda ke ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗa babban birnin tarayya da arewacin ƙasar, musamman jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da FRSC ta fitar, ta bayyana cewa:
“Cunkoson ya faru ne sakamakon hatsarin da ya haɗa da wata tanka a kusan kilomita biyu bayan Jere, kusa da ƙauyen Katari. Ana shawartar direbobi da su kasance masu lura da hanya, su bi dokokin hanya da kuma kaucewa tsallaka layi. Jami’anmu na FRSC suna wurin suna ƙoƙarin cire cikas domin dawo da zirga-zirga yadda ya kamata.”
Cunkoson ya kara dagula lamarin da jama’a ke fuskanta a titin, inda da dama daga cikin fasinjojin da ke kan hanyar sun nuna damuwarsu, suna koka da cewa aikin gyaran hanya da aka fara tun lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bai kammala ba har yanzu.
Wani fasinja da aka yi hira da shi ya ce:
“Mun makale sama da awa uku! Ba mu san lokacin da za mu isa ba.
KU BIYO MU A FACEBOOK