Rundunar Tsaron Najeriya ta Operation Safe Haven ta samu nasarar kama wasu barayin daji da kuma wanda ke sayar musu da bindigu da harsashi.
Wannan nasara ta biyo bayan samun sahihan bayanan sirri da suka ba da damar kai farmaki a maboyar miyagun.
A yayin samamen, an kama Yahaya Adamu, wanda ake zargin yana da hannu a satar mutane da kashe-kashe a yankin Barikin Ladi na Jihar Filato. Daga bisani kuma, an kama mai gidansa wanda ke sayar da makamai da harsasai mai suna Saeed Haruna.
Ana zargin su da hannu a wasu munanan laifuka a Barikin Ladi da kuma Fadan Karshe a karamar hukumar Sanga, Jihar Kaduna.
Sojojin sun tabbatar da ci gaba da farautar sauran ‘yan kungiyar, tare da tabbatar da hukunta su domin kawo karshen aikata laifi a yankin.