Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarnin daukar aiki kai tsaye ga ma’aikatan shirin kiwon lafiya a fadin kananan hukumomin Najeriya 774.
Sanarwar ta biyo bayan kiran Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Ali Pate, da ya bukaci dukkan matakan gwamnati su shigar da matasan cikin ma’aikatansu domin tallafawa samar da kiwon lafiya ga kowa.
Yayin da yake jawabi ga matasan da aka dorawa kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kananan hukumomi, Tinubu ya tabbatar da cewa “an dauke su aiki”, yana musu albishir da samun gurbin aiki bayan kammala wa’adinsu na shekara guda.
Shirin kiwon lafiyar Najeriya an tsara shi ne domin kawo sauye-sauye masu ma’ana ta hanyar kirkire-kirkire a bangaren lafiya. Ma’aikatan da aka zabo sun fito ne daga cikin 359,000 da suka nemi aikin, bisa cancanta.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X