Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano cikin shekara guda.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Sunday Dare, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware kuɗaɗen da za a yi amfani da su don kammala aikin da ya tsaya.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Dare ya ce a ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya amince da kasafin kuɗin da za a yi amfani da shi wajen kammala sassan titin da ba a gama ba, musamman daga Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Zaria, cikin watanni 12.
A baya, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kamfanin Julius Berger da ke aikin hanyar saboda tsaikon da aka fuskanta wajen kammala shi.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X