Majalisar wakilai za ta ci gaba da muhawara kan kudirin gyaran haraji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisar domin tantancewa da kuma amincewa.
A ranar 30 ga watan Nuwamban bara ne dai majalisar ta dakatar da muhawarar da ta ke shirin yi kan kudurorin har zuwa wani lokaci bayan suka da wasu sassan kudurorin da ’yan majalisar wakilai daga yankin arewacin kasar suka yi.
Kamar yadda a wancan lokacin gwamnonin jihohin Arewa ma suka yi kakkausar suka ga wasu sassan kudurorin, wadanda suka ce suna da nasaba da muradu da jin dadin al’ummar Arewa.
Sai dai wani dan majalisar daga daya daga Arewa Maso Yamma ya shaidawa manema labarai cewa, an shirya ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa kan kudirorin, kuma shi ne babban batun da ke gaban majalisar wakilai a zaman majalisar a yau, Laraba.
ko me majalisar wakilan zatayi a muhawara kan kudirin gyaran haraji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar domin tantancewa duba da yadda al’umar arewa ke ta cece kuce akan gyaran harajin
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X