Bisa damuwa kan yawan mace-macen dake faruwa a fashewar tankokin manfetur da sauran munanan haɗɗurran gobarar manfetur a kasar nan,shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi domin kawo karshen wannan masifa, data laƙume rayuka 265 daga watan satumba kawo yau.
Shugaban ƙasar ya dau matakin ne bayan gobarar fashewar wata tankar mai da ta laƙume mutane 88 a kwanar Dikko ta jihar Neja a daran ranar Asabar.
Yayin da yake koka wa game da rashin waɗan nan bayin Allah,shugaban ƙasa , ya kuma umarci Hukuomomin tsaron da suka dace da hukumar kare hadɗurra su haɗu suyi aiki tare domin kare sake afkuwar hakan a ko’ina a ƙasar nan.
Ya kuma umarci Hukumar wayar da kai ta ƙasar nan NOA ta fadakar da jama’a kan illar kwasar ganimar manfetur a duk lokacin da aka samu haɗɗarin faduwar tankar mai.
Ministan yada labarai da wayar da kai, Muhammad Idiris ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci wakilan gwamnatin tarayya domin yin ta’azzi yya ga mai girma Sarkin Suleja Alhaji Auwal Ibrahim a kan fashewar tankokin manfetur
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X