Mataimakin Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Mujahideen, ya bayyana cewa hukumar ta mayar da Naira miliyan 212 da 30 ga masu hakkinsu a shekarar 2024.
Ya ce kudaden da aka maida sun shafi rikice-rikicen kasuwanci, gado, da basussuka. Wannan nasara, a cewar sa, wani bangare ne na kokarin hukumar na tabbatar da adalci da kyautata zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Sheikh Mujahideen ya kuma jaddada cewa, karkashin jagorancin Sheikh Aminu Daurawa, Hukumar Hisbah ta kuduri aniyar cimma manyan muradu guda biyar a bana. Wadannan muradu sun hada da wayar da kan jama’a, rage talauci, gyaran tarbiyya, bunkasa sana’o’i da bayar da jari, da kuma hada kai da masu sha’awar zaman lafiya da ci gaba.
Hukumar ta kara tabbatar da aniyarta na ci gaba da aiki tukuru wajen kare hakkokin al’umma da inganta zaman lafiya a Kano.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X