Gwamnonin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga kudirin sake fasalin haraji da gwamnatin tarayya ta bullo da shi, sai dai sun gabatar da wani sabon tsarin gyaran haraji na VAT.
Hakan na zuwa ne bayan taron kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, da kwamitin shugaban kasa na gyara haraji wanda aka gudanar a ranar Alhamis.
Kungiyar gwamnonin, a cikin sanarwar da ta fitar a karshen taron, ta jaddada goyon bayanta kan sake fasalin dokokin haraji na Najeriya.
A cewar su, sabuwar dabarar rabon za ta kasance kashi 50 bisa dari za a raba dai-dai tsakanin jihohin, sai kashi 30% bisa la’akari da abin da jihohin suka samu, sannan kashi 20% bisa yawan jama’a.
Mambobin sun amince da cewa bai kamata a kara harajin VAT ko rage harajin Kamfanoni (CIT) ba a wannan lokaci, don tabbatar da daidaiton tattalin arziki.
NGF ta ba da shawarar cewa bai kamata a rusa Asusun Tallafawa Manyan Makarantu, TETFUND, da Hukumar NASENI, da Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa, NITDA, a cikin rabon harajin ci gaba a cikin kuɗaɗen.
Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne shugaban kasa, Bola Tinubu ya aike da wasu kudirori guda hudu na gyaran haraji ga majalisar dokokin kasarnan, inda ya bukaci ‘yan majalisar su duba su kuma amince da su.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X