Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankali tare da kai rahoton duk wani zargi na cutar murar tsuntsaye (bird flu) ga hukumomin da abin ya shafa.
Wannan kiran ya zo ne bayan samun rahoton wani matashi daga ƙaramar hukumar Gwale wanda Agwaginsa suka kamu da cutar. Gwajin da aka gudanar a asibitin dabbobi na Gwale ya tabbatar da cewa murar tsuntsaye ce ta kama Agwagin.
A sakamakon haka, ma’aikatar aikin gona ta rufe wurin, ta kashe sauran tsuntsayen da ke wurin, sannan ta tsaftace wuraren kiwo da kasuwanci a kasuwar Janguza, inda aka ce matashin ya sayo tsuntsayen.
Haka kuma, an wayar da kan masu sana’ar sayar da tsuntsaye game da hadarin cutar don hana yaduwarta. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya tabbatar da cewa ba a kai ga ɓarkewar cutar ba.
Ya ce ana daukar matakan gaggawa tare da haɗin gwiwar ma’aikatun aikin gona, muhalli, da albarkatun ruwa don kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.
Kwamishinan ya shawarci masu kiwon tsuntsaye su lura da alamun cutar kamar zazzabi da kumburin idanu a cikin tsuntsayensu, tare da daukar matakan kariya. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da wayar da kai da sanar da jama’a game da halin da ake ciki.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X