Gobara Ta Lalata Sama da Gidaje 10,000 a California, Mutane 7 Sun Mutu
Jami’ai a birnin Los Angeles sun ce mummunar gobarar daji ta lalata sama da gidaje dubu 10 da wasu gine-gine a jihar Californian.
Adadin waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu ya kai 7, ana kuma ci gaba da neman wasu.
Brad Sherman ɗan majalisa ne mai wakiltar Carlifornia, ya bayyana halin da ake ciki, inda ya ce wannan ce gobara mafi muni a tarihin Amurka.
Ya ce babu wanda ya taɓa tsammanin lamarin zai kai haka ga kuma iska mai ƙarfin da ake fama da ita na ƙara rura wutar. Ƙiyasin ɓarnar da wutar dajin ta yi ya tashi sosai zuwa aƙalla dala miliyan 135.
An tura jami’an tsaro na ƙasa 400 a yankin domin taimaka wa ‘ƴan sanda aikin, bayan da aka samu rahotanni sata ko kwashe kayan jama’a.
Da yake magana a wani taron manema labarai, babban jami’in ‘ƴansanda na birnin na Los Angeles, Jim McDonnell, ya ce abin da suka mayar da hankali yanzu a kansa shi ne kare aikata miyagun laifuka.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X