Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu, tsohon Shugaban Ma’aikata da Kwamishinan Kudi a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana tsohon gwamnan a cikin wani batun zargin halatta kudin haram.
Sa’idu yana zargin cewa ya sayar da dala miliyan $45 na gwamnatin Jihar Kaduna akan farashi mai rahusa na Naira 410 kan kowace dala, maimakon farashin kasuwar bayan fage na Naira 498. Wannan ciniki ya janyo asarar kusan Naira biliyan 3.96 ga jihar.
Wannan lamari ya faru ne a shekarar 2022 lokacin da Sa’idu ke matsayin Kwamishinan Kudi. A cikin wata bayani da ya yi wa ‘yan sanda, Sa’idu ya ce tsohon gwamna El-Rufai ne ya bayar da umarnin yadda za a sauya kudaden. Ya kara da cewa, tsohon gwamnan ne yake fitar da adadin kudin da za a sauya tare da amincewa da farashin da masu siye ke bayarwa, wanda yawanci ya fi na kasuwar bayan fage.
Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta gurfanar da Sa’idu a kotu bisa zargin aikata laifin halatta kudin haram bisa dokar Money Laundering (Prevention and Prohibition) Act, 2022. Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru hudu zuwa goma sha huɗu a gidan yari, ko tara wanda bai gaza sau biyar na kudin da ya shafi laifin ba, ko kuma duka biyun.
Har yanzu tsohon gwamna Nasir El-Rufai bai mayar da martani kan wadannan zarge-zarge ba. Ana ci gaba da shari’ar, yayin da aka shirya yanke hukuncin neman belin Sa’idu a ranar 16 ga Janairu, 2025.
LIKE & FOLLOW US ON FACEBOOK, X, INSTAGRAM, LINKEDIN & YOUTUBE