Yan sanda a Jihar Kano sun tsare wata amarya kan zargin kashe angonta ta hanayar bashi guba bayan mako biyu da ɗaurin aurensu.
Ana zargin amaryar ta kashe ango nata ne ta hanyar sanya masa maganin ɓera ne a cikin abincinsa.
Lamarin ya faru ne a unguwar Yakasai da ke birnin Kano a ranar Alhamis.
Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Haruna Kiyawa ya ce an garzaya da angon mai suna Umar Sani zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano inda a nan ne rai ya yi halinsa.
Kiyawa ya ce ya ce dangin ango me suka kai wa ’yan sanda ƙara a ranar Litinin, bayan faruwar lamarin.
Ya kara da cewa ko da ’yan sanda suka je gidan, amaryar ta riga ta cika bujenta da iska, amma daga bisani an yi nasarar kamata a ranar Laraba.
A halin yanzu tana tsare tana amsa tambayoyi a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar kafin a gurfanar da ita a gaban kotu.