Hukumomi a Koriya ta Kudu sun ce mutum 179 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman da ya auku a filin jirgin saman Muan ranar Lahadi da safe.
Mutum biyu kawai aka samu cetowa daga hatsarin – waɗanda dukkansu ma’aikatan jirgin ne da aka zaƙulo daga cikin baraguzan jirgin.
Hakan na nufin duka fasinjojin jirgin 175 haɗe da ma’aikatansa hudu sun mutu a hatsarin.
Jirgin ya kauce daga titinsa yayin da yake sauka a filin jirgin sama a Koriya ta Kudu.
Jirgin ƙirar Boeing 7-3-7 ya sauka kenan, bayan dawowa gida daga Bangkok na kasar Thailand, dauke da fasinjoji 175 da ma’aikatansa shida.
Saukar ta sa ke da wuya ne ya kwace ya saki titinsa ya kutsa ta cikin wani gini, kana ya kama da wuta.
Shaidu sun ce sun ji karar fashewar wani abu mai karfi bayan faruwar lamarin.
Wasu ɓangarorin jirgin sun ƙone ƙurmus yayin da baƙin hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar inda lamarin ya faru.
Har yanzu ba a san musabbabin faɗuwar haɗarin ba, amma kafofin watsa labaran cikin gida na bayar da rahoton cewa mai yiwuwa tsuntsaye ne suka shige cikin injin jirgin suka haifar masa da matsala.
Shugaban ƙasar na riƙo ya aike da saƙon jaje ga ‘yan ƙasar, tare da alƙawarta gudanar da bincike.
Hukumar sufurin ƙasar ta sanar da jigilar mutane a jiragen ƙasa kyauta zuwa wurin da lamarin ya faru.
Iyalai da ‘yan’uwan waɗanda lamarin ya shafa sun yi cincirindo a wajen filin jirgin saman cike da faragabar rasa ‘yan’wansu.