Bayan kada kuri’a a zaben shugaban kasa dana yan majalisu a tarayyan Najeriya, hukumar Zabe ta kasa ta fara fitar da sakamakon zaben da ya gudana a ranar asabar 26 ga watan fabrily shekarar 2023.
Jahar katsina wace daya ce a cikin jerin jahohin da jamiyar APC dakuma PDP ke sa ran samun kuri’u da dama daka shiyar arewa maso yanmacin Najeria.
Saidai alkaluma suna bayana dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, na jamiyar peoples democratic party (PDP) ya same kuri’u mafi rinjaye a jahar katsina.
Bayan kididiga da hukumar zabe ta kasa ta bayar kuri’un dan takarar jamiyar PDP, Atiku Abubakar sun dara na Bola Ahmed Tinub na jamiyyar APC mai mulki da kuru’u dubu shida da dari bakwai da situn da biyu 6,762.
Duk dacewa Tinubu yasama rinjaye a kananan hukumomi ashirin da daya sai dai yawan kuri’un da yasama masu adadi “dubu dari hudu da tamanin da biyu da dari biyu da tamanin da uku” (482, 283) ba su kai yawan na Atiku Abubakar ba, wanda ya sami kuri’u “dubu dari hudu da tamanin da tara da arbain da biyar” (489,045) a kananan hukumomi sha uku.
A dayan bangaren kuma, dan takarar shugaban kasa na jamiyar NNPP kuma tsohon gwamnan jahar kano, Rabi’u Musa kwankwaso ya sami kuri’u dubu sitin da tara da dari uku da tamanin da shida (69,386).
Malam Mu’azu Abubakar, baturen zabe a jahar katsina ne ya sanar da sakamakon zaben a shelkwatar hukumar dake jahar katsina.
LIKE & FOLLOW US ON FACEBOOK, TWITTER, INSTAGRAM, LINKEDIN & YOUTUBE