La’akari da kalubalen da ilimi ke fuskanta a arewacin Najeriya, kungiyar Universal Writers and Authors ta bazama wajen kalubalantar koma bayan da ilimin ke fama da shi, tareda inganta ilimi ta hanyar fiddo da sabbin tsare tsare ta hanyar shirya gasa a fanin rubutun zube da harshen turanci ga yara yan sakandare.
Kungiyar dai na shirya gasar ne shekara shekara domin tabbatar da yaduwar ilimi mai inganici wanda zai baiwa kowan ne bangare karin inganci da kuma kulawa ta musan domin ci gaban ilimi baki daya.
A gasar da kungiyar ta shirya a zangon karatu na shekarar 2022/2023 wanda aka yiwa lakabi da “UWA 2022/2023 English Language Competition” Makarantar Olive International Schools ce ta yi nasarar lashe ta a zagaye na farko wanda aka kammala ranar 19 ga watan Faburairun shekarar 2023.
Da ya ke tofa albarkacin bakin sa bayan kammala gasar a jahar kaduna, shugaban kungiyar Malam Abdulazeez Alhassan ya nuna farin cikin sa akan yadda daliban makaratun da suka fafata a gasar suka nuna hazaga da kuma gogewa wajen amsa tambayoyi duk da karancin shekaru da da wasu dalibai ke shi a garsar harshen Turanci.
“Lalai wannan ya nuna cewa dukanin gasar da muke shirya wa a duk shekara na kara inganta ilimi da kuma kwarewar malamai da dagewar masu makarantu don ganin dalibai ko yaran gobe sun sama ilimi mai inganci a arewacin najeriya.”
“Duba da sakamakon gasar inda makarantar Olive International ta samu maki mafi yawa har ta yi nasara lashe na daya a zagayen farko, ya yin da kuma Iman Academy da Salfanamoh College da Iman Exclusive da Kuma Iman International suka zo mataki na 2, 3, 4, da kuma 5.”
“Sakamakon ya tabbatar da cewa kokarin da muke yi a kungiyar Universal Writers and Authors na kalubalantar koma bayan ilimi a yankin arewacin Najeriya na samun nasara matuka.”
“Hakan kuma zai kara mana hazaka da zage damtse wajen ganin yaran da basa zuwa makaranta sun koma tareda baiwa makarantu da malamai horo wajen samar da ilimi mai inganci domin jama’a da kasa su amfana.”
“Kafin wannan lokacin, a kungiyar mu, ko yaushe muna cikin baƙin ciki sabida karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta da ƙarancin bada ilimi mai inganci a makarantu da dama; daya daga cikin dalilin da ya Kara karfafa mana gwiwa wajen dagewa don tabbatar da ingantaccen ilimi ta re da sake farfado da martabar karatu da rubutu da aka rasa a tsakanin ɗaliban da kuma makarantun sakandare.”
“Duk da cewa muna gode wa ma’aikatar ilimi ta Jihar Kaduna bisa yadda ta ke shiga shirye-shiryen mu a kullum don ganin mun cimma manufofin mu na inganta ilimi, amma akwai bukatar gwamnatoci da sauran hukumomin da abin ya shafa, musamman kungiyoyin farar hula, su hada kai da tallafa wa ayyuka irin namu.”