Daga: Aliyu Dahiru Aliyu
A duk lokacin da kaga wani mutum mutane sun rabu gida biyu a kansa, tsakanin mai kambamashi har ya kaishi matsayin allantaka da kuma mai zaginsa ya mayar da shi tamkar shedan; ka tabbatar akwai ababan izina a rayuwar wannan babban mutum da ya kamata a lura da shi duba na tsanaki.
Sheikh Ibrahim Inyass ya rabu gida biyu a gurin musulmin yammacin Afrika tamkar yadda Sayyidi Ali ya rabu tsakanin “ghullatus Shi’a” masu allantar da shi da kuma Banu Umayya masu zaginsa. Tamkar Annabi Isa (as), tsakanin yahudawan da suka yi zaton sun kasheshi da kuma kiristocin da suka allantar da shi.
Wani abu da ya janyo mutane suka rabu gida biyu a kansa yana da alaka da yanayin kalaman sufancin da yake da salon irin su Abu Mansur Alhallaj da kuma Sheikhul Akbar Ibnul Arabiy da mutane suka rabu a kansu, tsakanin masu ganinsu a manyan zindikai da kuma masu daukansu manyan waliyyai. Haka kuma maganganun manyan litattafan da suke dadewa a tarihi suke cike da tauriyyar da mutane suke yi musu fahimtu mabanbanta.
Alqur’ani, Bible, Torah da Vedas sun dade a tarihi ne kuma suna daukan mabanbanta zamani da mabanbantan guri saboda suna daukan sharhi da fassara daidai juyawar zamani. Da litattafan sun yi magana zallanta da ba wani surkuki a ciki da canjin zamani zai tafi da su ne. Alqur’ani a misali zaka tarar yana fuskoki dayawa ta yadda kowa yake da fassararsa ta daban akai. Masu neman zaman lafiya da yan ta’adda kowa gani yake Alqur’ani goyon bayansa yake!
A takaice dai Sheikh Ibrahim Inyass zai dade tarihi bai manta da shi ba. Kuma zai tafi tsakanin masu ganinsa malami kawai da masu ganin shi allah ne baki daya! Wasu kam kallon shedan za su dinga yi masa. Rayuwar Sheikh Ibrahim irin ta manyan mutanen da ake rarrabuwa akansu ce. Kowa da fuskar da yake ganinsa. Wannan ta sa Sheikh Ibrahim ya zama babban mutum.
Yardarka da Shehu Ibrahim ita tasa ya zama babban mutum. Rashin yardarka da shi ita ta kara tabbatar da babban mutum ne. Tarihi zai dade yana ambatonsa.