A ranar jumma’a 21 ga watan Jaunuary 2022 ne da karfe 2: 12 na rana, shi DCP Abba Kyari ya kira daya daga cikin jami’an NDLEA a garin Abuja.
Bayan minti biyu kiran Sai shi jami’in ya rama kiran da yayi masa, sai Kyari yace masa zai zo wajensa bayan sallar jumma’a don su tattauna wata magana da ta shafi aiki.
Sai suka hadu a wajen da suka shirya haduwa kuma kai tsaye shi Abba Kyari ya fara bayani, wanda shi ne:
Yaransa sun kama Wasu masu safaran miyagun kwayoyi da suka shigo kasarnan daga Ethipia dauke da 25kg na cocaine.
Abinda yake so shi ne, shi da yaransa zasu dauki 15kg su bar 10kg wanda dasu ne za ayi amfani wajen gurfanar da wadannan masu safara a koto a Enugu inda aka kama su.
Sannan kuma 15kg da shi da yaransa zasu daukan za a maye gurbinsu da cocaine na boge na daidai yawan wanda aka ciren, wato 15kg yanda baza a gane ba.
Abinda yake so da wannan jami’in na NDLEA shine ya taimaka wajen shawo kan Manyansa na ofishinsu dake nan FCT (Abuja) da su yarda da wannan shiri nasa.
Da karfe 11:05 na ranar Monday 24 ga watan January bayan hukumar ta bashi izininin nuna wa Abba Kyari cewa sun yarda da shirinsa ne Sai jami’in da Abba Kyari suka ci gaba da yin video call ta WhatsApp a gaba daya wannan rana inda ya fada masa cewa an yarda suci gaba da wannan harkalla.
Daga nan ne Abba Kyari ya fada masa cewa har sun raba 15kg na cocaine din da suka dauka tare da informant din da suka kawo masu labarin wadannan masu safara. Inda sun bada informants din 7kg shi kuma da yaransa sun dauki 8kg har ma sun sayar da nasu kason.
Daga nan ne sai ya ya ce yana so shima wannan jami’in da mutanensa na FCT command su ci moriyan wannan harkalla, inda ya ce in sun yarda zai sayar da 5kg daga cikin wancan 10kg da ya rage ya kawo masu kudin. Sai ya rage 5kg kawai na zallan cocain za a kai kotu sauran kuma a sa na boge.
Tunda ana sayar da kowane gram na cocaine Milliyan bakwai to kudin da zai kawo masu akan wannan 5kg zai zama naira 35 million kenan a dala kuma $61, 400 kenan.
Daga nan ya matsa wa jami’in cewa ya kamata hukumarsu na Abuja su karbi su wadanda ake tuhuma da kuma sauran cocaine din daga hannunsu tunda suna nan a Abuja. Shi kuma yace yana wayan ne daga Legas inda yaje wata harka ta kansa.
Washegari January 25th Abba Kyari yace zai turo Kaninsa da ya kawo kudin wa jami’in, yaransa kuma su kawo masu laifin tunda baya nan, amma jami’in yace a’a ya fi so ya hadu da shi ba wani ba.
A wannan rana da karfe 5:23 bayan ya dawo suka hadu a wajen da suka fara haduwa.
A cikin tattaunawarsu ya fada masa yadda suka sami labarin miyagun daga wajen wani Sawun-keke wanda yake tare da miyagun kuma yana tare da shi Abba Kyarin daga nan ne yaransa suka tashi zuwa Enugu suka kama wadancan.
Ya kuma ce a bisa umarninsa ne take suka cire 15kg din suka maye gurbinsu da na boge, kuma suka yi shaida akan na gasken yadda in an zo gwaji za a gane su.
Ya fada masa yadda in an kawo cocaine din NDLEA za a gane 5kg din da suka rage wanda sune asalin cocaine din, za a gansu da digon ja. Saboda kar a zo yin test din gane asalin cocaine kuma a dauko na boge.
Ya kuma tura wa jami’in hoton pakitin 5kg din da ya rage yadda zasu gane. Aka kuma shirya cewa 5kgn shi kadai za a dauka a gwada, tunda ana ganin cocaine ne ba Sai an taba sauran na bogin ba.
Ya kuma kawo kudin wadancan cocaine 5kg da suka sayar a madadin NDLEA wato dala 61, 400 amma jami’in yace ba zai karba a waje ba Sai a cikin mota. Daga nan ne suka shiga mota wacce an riga an sa na’urar daukan magana da na video inda ake jinsa yana bayani da bakinsa akan harkallan.