">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Thursday, October 16, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

RAYIWAR YAN AREWA A KUDU

by Abubakar Ismail kankara
February 7, 2022
in Art, Ra'ayi
0
RAYIWAR YAN AREWA A KUDU
Share on FacebookShare on Twitter
">

RelatedPosts

Yan Arewa Masu fataucin kayan abinci sun Fara kai Kaya kasahen Burkina Faso da Cote d Ivoir

">
RAYIWAR YAN AREWA A KUDU
Daga: Sabo Ibrahim Hassan
">

Da farko kamar bazanyi rubutu game da wannan abin da ya daɗe yana cimin tuwo a ƙwarya ba, dalili kuwa shine, waɗanda zanyi dansu ba karantawa zasuyi ba kuma ba lallai saƙon ya isa garesu ba saboda mafi yawancinsu basu ma san ina suka sa gaba ba.

A ƴan shekaru huɗu da Allah yabani damar zuwa wasu garuruwa na kudancin Najeriya, na haɗu da mutanenmu matuƙa, hasali ma duk inda naje mutanenmu nake fara neman inda zan samu, dan inji labarin gari da kuma yadda rayuwa take a garin.

 Babban abinda yafi bani takaici ya ɓata min rai shine, yawancinsu sana’oi suke na ƙasƙanci wanda kuma idan mutum na da lafiyar lissafi yasan ba wani abu da wadannan harkokin zasu tsinanawa mutum a irin wannan rayuwar da muke ciki. Yadda Allah ya albarkaci wannan yanki na Arewacin Najeriya da abubuwa na sana’a masu tarin yawa sai ka rasa hau ne ko rashin hankali ne ke kai wasu zuwa kudancin Najeriya dan nema.

Ko da cewa yawancinsu mutanen ƙauye ne, amma na fahimci rashin wayar da kai da kuma mahimmanta kai shine asalin abinda ke kaisu irin wannan guraren. Daga masu babur, sai masu yankan farce, sai masu amalanke, sai kuma masu aiki na dako. Ba sana’oin bane damuwata, shin sun rasa wajen irin wannan sana’oin ne a Arewa?

Irin wulaƙanci da rainim hankali da ake musu shine yafi sosa min rai.. Mutannennan suna da Iyaye, wasu na da Iyalai, amma sai karasa wani lissafi ne zai sa mutum yabaro cikin yan’uwansa da suke a watse cikin Jahohi sha tara na Arewacin Najeriya.

Na fahimci wani abu ɗaya a hirar da nayi da mutane mabanbanta, yawancinsu abinda ke musu daɗi da zaman irin wadannan garuruwan zallar son bariki ce da kuma tsantsar ƴanci ba mai hanaka ba mai sa ka.

Inda zuwa ne dan kai wata Haja, ko yin wata sana’a mahimmiya wannan lamarine na sambarka, amma yadda ake kwasarsu a jibga su a motar Shanu su tafi a wulakance haka yawancinsu ke dawowa.

Lallai yana da matuƙar mahimmanci duk inda muka haɗu da masu irin wannan baragubin tunanin mu dinga wayar musu da kai, kuma mu nunar musu illa da rashin makoma mai kyau dake tattare da haka.

DAILY EPISODE HAUSA
KUBIYO MU A FACEBOOK & TWITTER
RAYIWAR YAN AREWA A KUDU
Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

Yan Arewa Masu fataucin kayan abinci sun Fara kai Kaya kasahen Burkina Faso da Cote d Ivoir

Yan Arewa Masu fataucin kayan abinci sun Fara kai Kaya kasahen Burkina Faso da Cote d Ivoir

by Abubakar Ismail kankara
February 27, 2021
1

Rahotanni daga iyakokin Nageriya ya nuna Cewa Masu fataucin kayan abinci daga Arewa zuwa kudancin Najeriya sun fara komawa fidda...

Next Post
yan bindiga

An Kashe Shahararren Dan Ta’adda Gwaska, Yayin Da Mazauna Yakin Yantumaki Ke Hijira Kan Tarar N30m Da Barazanar Kisa

yan fashi da garkuwa da mutane

Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga 20 Dasukayi Yunkurin Kai Hari NDA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In