Jamil Ismail Mabai, haifaffen Katsina dan jarida mai zaman kansa kuma mawallafin jaridar Click, yayi nasarar shiga cikin jerrin yan jarida da aka zaba don karamawa ta Gatefield’s People Journalism Prize for Africa 2021 Nominees.
A cewar PJPA, Jamil dan jarida ne mai zaman kansa wanda labaransa suka bankado ta’asar da ake yi a yankin Arewa maso Yamma a Najeriya dukda hatsarin da ke tattare da shi.
Mabai, wanda shi ne dan jarida na farko daga Katsina da Arewacin Najeriya da aka zaba, an zabe shi ne a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan jarida wadanda suka kware wajen aiki tukuru ba tare da gajiyawa ko tsoro ba, kuma suka bankado tare da fallasa boyayyun gaskiya da ke faruwa a yankin Arewa maso Yamma da yake fama da matsalar matsalar tsaro dakuma koma baya wajen cigiban kasa..
Garfield-backed People Journalism Prize for Africa (PJPA) karamawace dake tallafawa da karama yan jarida da masu kare rajin bil’adama a nahiyar africa.
Ko da yake wannan ita ce shekara ta 3, da ita PJPA ta karrama ‘yan jarida, masu kare hakkin bil’adama, da masu kare rajin dan adam da dai sauransu, a Afirka bisa ayyukan sadaukar da kai a fannonin sana’o’insu daban-daban.
Sauran wadanda aka zaba daga Najeriya sun hada da Laila Johnson Salami, Samuel Ogundipe, Sandra Ezekwesili, da Irene David-Arinze, yayin da Daneel Knoetze/View Finder (Afirka ta Kudu), Naipanoi Lepapa (Kenya), Manasseh Azure Awuni (Ghana), Lucy Kassa (Ethiopia) , da Elizabeth Merab (Kenya)
Ana sa ran za a bai wa wadanda suka ci kyautar Gatefield’s Journalism Prize for Africa kudi dala $1,500, jimlar dala 3,000 a matsayin ladan kudi ga ‘yan jarida da suka yi nasara.
KUBIYO MU A FACEBOOK & TWITTER