Abubakar Kawu Baraje ya gano asalin matsalar rashin tsaro a kasar zuwa kwararar Fulani daga kasashe makwabta kamar Saliyo, Mali, Senegal, Niger da Chadi da aka shigo da su kasar domin gudanar da zaben a shekarar 2015.
Ya fadi haka ne a Ilorin a wani bangare na ayyukan cika shekaru 70 da haihuwa.
Ya kuma goyi bayan shirye-shiryen taimakon kai da kai da gwamnonin kudu maso yamma suka yi, inda ya bayyana cewa martanin da Sunday Igboho ya yi wa lamarin makiyaya ya zama dole saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza a babban nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyi.
Baraje ya ce jam’iyya mai mulki bata lokaci ne kawai.
A cewar tsohon shugaban na PDP, wanda kuma ya taba yin sakataren jam’iyyar na kasa, shugaban bangaren da ya balle na PDP wanda ya kafa ginshikin jam’iyyar mai mulki a yanzu, mazajen Fulani da ke haddasa fitina a kasar ba ‘yan asalin Najeriya ba ne.
“Ba tambayar da ta dace muke yi ba kan yadda Fulanin da muke rayuwa tare da su suka zama hatsari kwatsam.
“Dole ne kuma mu nemi yadda suka yi amfani da bindigoginsu,” tsohon shugaban jam’iyyar ya tambaya.
Baraje ya ce bafulatanin da ke yin barna a kasar ba Fulanin Najeriya ba ne. “Hukumomin tsaro ba su bude baki kan yanayin matsalar ba.
Weldon, mun gode
I Allah ba’a zalumin koba
Ashe kune kuka kawo mana matsala a Najeriya