Dokta Hussaina, Daya dakacikin yayan tsohon gwamnan jihar Gombe wato Sanata Danjuma Goje tayi murabus amatsayin Kwamishinar bayan zargin an kaima Mahaifinta hari.
Dokta Hussaina wace itace Kwamishinar Muhalli da Gandun Daji a Jihar Gombe ta mika takadar ajiye aikinne a ranar sabar.
Hakan yabiyo bayan wasu rade rade dake nuni dacewa a samu sabani tsakanin mahaifinta Sanata Danjuma Goje dakuma Gwamnar Jihar Gombe wato Gwmana Inuwa Yahaya.
A ranar Juma’a ne wasu yan bangar siyasa suka tare hanya kuma suka hana Sanata Danjuma shiga jihar ta Gombe wanda hakan yakaiga barkewar rikici tsakanin bangarorin na siyasa.
Wasu daka cikin magoya bayan Sanatan suna zargin bangaren gwamnatin da yinkurin hana shi shiga cikin birin Jihar ta Gombe.
Daka bisani anga sanatar tareda diyar tashi a saman bene yayinda yakewa magoya bansa godiya.
KUBIYOMU A FACEBOOK DA TWITTER