Tsohon shugaban majalisar dattawan Najariya Bukola Saraki ya ce, bai kamaata a barwa jam’iyyar APC mai mulki matsalar Najeriya ba ita kadai.
Saraki wanda shi ne ke jan ragamar kwamitin sasantawa na jam’iyyar PDP, ya nuna cewa a kwai bukatar hada hannu da ‘yan hamayya domin lalubo mafitar da za a yi maganin matsalolin Najeriya baki daya, musammam a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Saraki ya bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo a dakin karatunsa na Abeokuta da ke jihar Ogun.
Tsohon shugaban Majalisar ya ce, “Idan muna maganar akan garkuwa da mutane, abin da ake bukata shi ne gwamnati da samar da shugabancin da zai kira wo duka masu ruwa da tsaki. mu zo a tattauna muga yadda za a shawo kan wannan matsaloli.”