‘Yan bindiga sun sace mutum 60 a Zamfara.
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun yi garkuwa da gwamman mutane bayan wani hari da suka kai a ƙauyen Rimi da ke Ƙaramar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara ranar Juma’a.
Kwamishinan Yaɗa Labarai Ibrahim Dosara ya tabbatar da kai harin, yana mai cewa kusan mutum 60 ne ‘yan bindigar suka sace, amma ya ce ba a tabbatar da adadin ba tukunna.
“A safiyar yau [Juma’a] mun tashi da labarin cewa ‘yan fashi sun afka wa ƙauyen Rimi sun sace mutum 60, duk da cewa ba a tabbatar ba,” kamar yadda ya faɗa wa gidan talabijin na TVC.
Ya ƙara da cewa “jami’an tsaro da na gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da ainahin adadin mutanen da kuma waɗanda aka ji wa rauni”.
“Bakura hanyar ɓarayi ce wadda ta dangane da Dansadau zuwa Birnin Gwari [a Jihar Kaduna] da kuma wasu sassa na Jihar Neja,” a cewarsa.
A ranar Litinin da ta gabata wasu ‘yan fashin suka sace ɗalibai da malami da kuma iyalan malamin daga kwalejin harkokin noma ta garin na Bakura.