Jam’iyyar Adawa Ta PDP Ta Gudanar Da Taron Wayar Da Dakan Al’umma Gameda Rijista Zama Dan Jam’iyyar A Yanar Gizo.
Jaridar Dailyepisode ta ruwaito labarin da safiyar yau Asabar ne aka gudanar da gangamin taron kaddamar da shirin sabunta katin jam’iyyar PDP wanda ake yi yanzu haka ta kafar sadarwa, wanda ake kira da e-registration.
An gudanar da taron ne a karkashin jagorancin shugaban matasan jam’iyyar PDP na yankin Arewa maso yamma (north-west), wato Hon. Hamza Yunusa Jibia.
Sai kuma uban taro, kuma shugaban jam’iyyar PDP, sannan wakilin tsohon gwamnan jihar Katsina Barr. Ibrahim Shehu Shema, wato Hon. Salisu Yusuf Majigiri. Shima ya halarci wannan taro mai albarka.
Tare da sauran manyan masu rike da mukamai, da tsaffin ‘yan takara na kujeru daban~daban na jam’iyyar PDP. Duk sun halarci wannan taro.