Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar kowanne dan kasar Afghanistan ya samu damar walwala tana mai cewa ba ta bukatar abokan gaba.
Kakakin Kungiya Zabihullah Mujahid, ne ya shaidawa manema labarai a birin Kabul.
Zabihullah Mujahid ya bayyana a gaban ‘yan jarida a karon farko tun bayan da suka kwace iko a kasar, ya ce sun ‘yantar da kasar “bayana shekaru 20 na fafutika kuma mun kori ‘yan kasashen waje”.
“Wannan lokaci ne na alfahari,” in ji shi.
“Muna son tabbatar da ganin Afghanistan ba ta sake tsunduma cikin yaki ba. Mun yafe wa dukkan mutanen da suka yake mu. Gaba ta zo karshe, ” a cewarsa Mujahid.
Koda ya amsa tabayar wata yar jaridar Aljazeera, akan yancin mata da kuma walwalarsu, yace mata zasuyi aiki kuma zaabasu hakinsu , haka zalika zasuyi karutu anma saidai yace dole sai sunbi dokoki adinin musulunci.
Yakara da cewa dukan gidajen jaridu, officishin jakadanci na kasashe da kungiyoyin jin kai nada damar cigabada aiyukansu kana kuma zasu basu kariya don ganin ba’á cutar da su ba.