Shugabannin Kungiyar Hadin Kan Abinci da Dillalan Shanu na Najeriya (AUFCDN) sun dauki matakin toshe duk wata hanyar da ke hade arewacin Najeriya da kudu.
An dauki matakin ne bayan kungiyar kwadagon ta yi zargin kashe-kashe da lalata kadarori da kasuwanci ta yankin kudancin kasar.
Kungiyar kwadagon ta bukaci adalci da biyan diyya daga gwamnatocin sannan kuma ta bukaci kariya don faruwar abin daka iya janyo nadama nan gaba.