Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mashawarci na musamman ga Shugaban Kasa kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina, ya ce Shugaba Buhari ya fi son zuwa Birtaniya a duba lafiyarsa ne don likitocin Nijeriya ba su da bayanansa na lafiya.
An ruwaito cewa Adesina ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya kan dalilin da yasa Buhari ba ya yarda likitoci su duba shi a Nijeriya yayin wani shiri a gidan talabin na Channels Television.
A cewarsa, likitocin Birtaniya ne kadai suka da bayanan lafiyar Buhari. Fiye da shekaru 40 dama likitocin Burtaniya ke duba Buhari, Adesina Ya kara da cewa tun kimanin shekaru 40 da suka gabata likitocin na Burtaniya ne ke duba lafiyar shugaban kasan.
Ya ce: “Shugaban kasar ya dade tare da likitoci da tawagar masu kulawa da lafiyarsa fiye da shekaru 40. “Abin da ya fi dacewa shine ya cigaba da wadanda suka san bayannan lafiyarsa shi yasa ya ke zuwa Landan don ganinsu.